in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar za ta tanadi wani kundin shirin yaki da sigari
2014-07-25 10:01:33 cri

Wani gungun 'yan majalisun dokokin kasar Nijar dake yaki da sigari ya gudanar da wani zaman taro a ranar Alhamis a zauren majalisar dokokin kasar domin amincewa da wannan kundin shirin yaki da sigari.

Kundin da ma'aikatar kiwon lafiya ta Nijar ta sake farfado da shi, an gabatar da shi ga kwararrun yaki da sigari a Nijar.

A cewar darektan kula da tsabtar jama'a da ilimin kiwon lafiya a ma'aikatar kiwon lafiyar jama'a ta kasar, Harouna Yaro, kasar Nijar ta sake farfado da wannan shirin yaki da sigari bisa dalilin banbance banbance da ake samu wajen girmama matakai da dokokin da aka cimma a wannan fanni.

Wannan kundi da zaran ya samu amincewa, to zai taimakawa Nijar samun wani shirin da bangarori suka cimma, kana da hadin kai wajen yaki yadda ya kamata da wannan annoba ta sigari, in ji shugaban kungiyar yaki da sigari SOS-Tabagisme-Niger, malam Maiga Djibo Ibrahim. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China