in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bullo da sabuwar hanyar takaita yaduwar zazzabin cizon sauro
2015-03-25 10:28:55 cri

Masanan cibiyar binciken halittar kwari ta kasa da kasa (ICIPE) dake birnin Nairobi, sun gano wata sabuwar hanyar da za ta taimaka wajen sanya ido kan yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika.

Mista Mike Okal, wani masani a cibiyar ICIPE, ya bayyana cewa, wasu sinadaran halitta a sansanonin da sauro ke yaduwa kusa da tafkin Victoria, wato sinadarin Cedrol na jan hankalin macen sauro mai dauke da cutar zazzabin sauro, kuma da za a iyar amfani da shi wajen hada tarko domin janyo hankalin matan sauro, sannan a kashe su, ta haka za a hana yaduwar matan sauro kafin su kyankyashe kwayakonsu.

A tsawon shekaru shida na baya bayan nan, mun yi nazarin yawancin hanyoyin da nau'o'in sauro ke bi domin yada cutar zazzabin cizon sauro daga wurare daban daban, inda suke ajiye kwayakonsu, tambayar ita ce idan wannan shirin za a iyar amfani da shi domin kama da kashe matan sauro daban daban kafin su nasa darururan kwayakwai, to hanya ce mai kyau, in ji mista Okal

Masana da dama sun bullo da irin wadannan sinadirai na korar ko janyo hankalin matan sauro masu dauke da cutar zazzabin cizon sauro, amma duk da haka wannan ne karon farko da aka sami wani sanadarin ta hanyar bincike da aka tabbatar da shi dake jan hankalin macen sauro a lokacin da take neman wurin da za ta nasa kwai.

Wadannan bincike na samar da wata sabuwar hanyar sanyo ido kan sauro, kuma za su taimaka wajen karfafa kokarin sanya ido kan cutar zazzabin cizon sauro a yankunan kasashen Afrika dake fama da wannan cuta, in ji mista Okal. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China