in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya na bisa hanya mai kyau wajen kawar da zazzabin cizon sauro
2014-10-14 13:41:19 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana a ranar Litinin cewa, kasar Kenya a yanzu haka tana bisa hanya mai kyau wajen kawar da zazzabin cizon sauro. Wakiliyar WHO dake kasar Kenya, madam Custodia Mandlhate ta nuna a yayin wani dandali kan zazzabin cizon sauro a birnin Nairobi cewa, an samu ci gaba sosai bisa kokarin karfafa ayyukan yaki da zazzabin cizon sauro. Ana ganin cewa, kashi uku cikin kashi hudu na al'ummar Kenya na zaman rayuwa a yankunan da ke fama da cutar da zazzabin cizon sauro, kuma masu kamu da cutar bai kai kashi biyar cikin dari ba, a wajen kananan yara 'yan kasa da ba su kai shekaru biyar da haifuwa, in ji madam Mandihate a yayin zaman bude taron kasar karo na biyu kan yaki da cutar malaria a kasar Kenya. Zaman taron na kwanaki biyu ya tattara masu fada a ji da kwararru fiye da dari biyu domin bunkasa yin amfani da bincike da shaidun kimiyya kan batun zazzabin cizon sauro.

Kasar Kenya ta sanya burin rage mutuwar jama'arta sakamakon zazzabin cizon sauro da kashi biyu cikin uku nan da shekarar 2017. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China