in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta yi maraba da ci gaban da aka samu wajen kyautata matsalar yara a Chadi
2016-06-29 12:56:59 cri

An samu ci gaba da dama a wadannan shekaru na baya bayan nan, domin kyautata matsalar kananan yara a kasar Chadi, amma har yanzu akwai sauran aiki, in ji Bakary Sogoba, shugaban tsarin kiyaye yara na kungiyar UNICEF dake Chadi a ranar Talata.

Tsakanin shekarar 2010 da shekarar 2015, adadin mace macen kananan yara ya ragu daga 106 a cikin haifuwa 1000 zuwa 72 a cikin haifuwa 1000, in ji mista Bakary Sogoba.

A cikin wannan lokaci guda, adadin yaran da aka yi allura ya karu daga kashi 8 cikin 100 zuwa kashi 25 cikin 100, kuma adadin yaran dake barci cikin gidan sauro ya karu daga kashi 12 cikin 100 zuwa kashi 36 cikin 100.

Idan aka dubi wadannan alkaluma, wajibi ne mu gaggauta kyautata yanayin da miliyoyin yara maras galihu da kuma rauni ke ciki, domin kaucewa sanya makomarsu cikin hadari, kuma daga bisani makomar kasar Chadi ita kanta, in ji jami'in na UNICEF. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China