Lu Kang ya ce, bayan da al'amura suka sauya a Sudan ta Kudu, Sin ta tattauna da masu shiga tsakani kan batun Sudan ta Kudu, da kokarin tabbatar da sulhu tsakanin bangarorin kasar Sudan ta Kudu, domin sa kaimi ga bangarorin da su tsagaita bude wuta da farfado da yin shawarwari tsakaninsu cikin hanzari.(Fatima)