in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban gungun yankin manyan tafkuna ya dauki niyyar yaki da 'yan tawayen RDC-Congo
2016-08-10 09:49:27 cri

Sabon sakataren zartaswa na taron shiyyar Grands Lacs wato manyan tafkuna (ICGLR) Zachary Muburi Muita, ya dauki niyya a ranar Talata na ci gaba da yaki da tsagerun dakarun dake da sansani a kasar RDC-Congo.

Gabashin RDC-Congo na kasancewa cikin zaman dar-dar dalilin wadannan dakaru. Tare da babbar gudummowar gamayyar kasa da kasa ta hanyar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake RDC-Congo (MONUSCO), da rundunar ko takwana da kuma rundunar sojojin Congo (FARDC), wadannan miyagun dakaru za a murkushe su, in ji Muita.

Kungiyar 'yan tawayen M23 tuni an shigar da ita cikin runduna, kuma ana ci gaba da kwashe tsoffin 'yan tawayen M23, in ji jami'in.

Ta wani bangare, mista Muita ya nuna cewa, aikin warware matsalar Burundi ya kai wani muhimmin mataki.

An samu ci gaba sosai a shawarwari na tsakanin al'ummar Burundi. Gamayyar kasashen gabashin Afrika (CAE) na sahun gaba kana ICGLR na kasancewa wani babban tallafi, in ji mista Muita.

A cewar wannan jami'i, wani dandalin shugabannin kasashen CAE zai gudana daga ranar 17 zuwa 18 ga watan Augusta a birnin Dar es Salaam, bisa burin yin nazarin wani rahoto da aka kammala kan ci gaban da aka samu na tattaunawar tsakanin 'yan kasar Burundi.

Zagaye na biyu na ci gaban tattaunawa tsakanin 'yan kasar Burundi da ya gudana daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Juli a birnin Arusha na kasar Tanzaniya bai taimaka ga cimma wata jituwa ba tsakanin gwamnatin Burundi da 'yan adawa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China