in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin shirya wasannin Olympics yana da kwarin gwiwa game da sha'anin kiwon lafiya a wasannin Olympics na Rio
2016-05-26 10:01:39 cri
Nan da watanni 2 masu zuwa ne, za a bude gasar wasannin Olympic ta birnin Rio. Sai dai gabanin hakan cutar Zika ta barke sakamakon cizon wani nau'in sauro dake yaduwa a kasar Brazil. A sa'i daya kuma, ganin yadda jihar Rio ta kasar Brazil din ke fama da matsalar karancin kudade, a wasu asibitocin gwamnatin yankin, inda ta kai ga an rufe wasu sassan ba da jinya.

Wadannan matsaloli dai sun haifar da damuwa ga jama'a, game da sha'anin kiwon lafiya yayin gudanar da gasar Olympics ta birnin Rio.

Bisa labarin da shafin Intanet na gasar wasannin Olympics ta Rio ya fitar, an ce, a kwanakin baya yayin da ministan kiwon lafiyar Brazil Ricardo Barros ke ganawa da jami'an kwamitin wasannin Olympics na duniya a birnin Geneva da ke kasar Switzerland, ya ce birnin Rio zai dauki likitoci 6,000 don ba da tabbaci game da sha'anin kiwon lafiya, don haka kwamitin wasannin Olympic na da kwarin gwiwa game da birnin ta fuskar kula da lafiya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China