in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Turkiyya ta gabatar da dokar kwaskwarima ga rundunar soja
2016-08-01 13:19:53 cri
A jiya Lahadi, majalisar ministocin Turkiyya ta ba da dokar yin kwaskwarima ga rundunar sojan kasar.

Dokar ta shelanta cewa, ma'aikatar tsaron kasar zata jagoranci rundunar sojan kasar, data sojojin ruwa, da ta sojin sama kai tsaye. Kuma mataimakin firaministan kasar, da ministan harkokin waje, da ministan shari'a, da ministan harkokin cikin gida na kasar za su halarci taron kwamitin soja bisa matsayin koli a kowace shekara.

Dadin dadawa, dokar ta sanar da rufe duk makarantun aikin soja a kasar Turkiyya, a maimakon haka, za a kafa wata sabuwar makarantar tsaron kasa a karkashin jagorancin ma'aikatar tsaron kasar. Ma'aikatar kiwon lafiya za ta jagoranci duk asibitocin rundunar soja kai tsaye a duk fadin kasar a maimakon rundunar soja, ciki har da makarantar Gulhane.

Bisa wannan doka, an kori sojoji 1389 bisa zarginsu da laifin yunkurin juyin mulkin da bai cimma nasara ba, ciki har da tsohon babban mai ba da shawara kan aikin soja na shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan, Ali Yazici, da tsohon mai ba da shawara na babban hafsan hafsoshin rundunar soja Hulusi Akar, Levente Tercan.

Kafin wannan, firaministan kasar Turkiyya, Binali Yildirim ya sanar da cewa, ma'aikatar harkokin cikin gida za ta jagoranci sojoji da kungiyar tsaron gabar teku a maimakon rundunar soja, yayin da za a rufe sansanonin rundunar sojan sama da wurin kwana na sojoji da dakaru masu adawa da gwamnati suka taba yin amfani da su a birnin Ankara da Istanbul.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China