in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar firayin ministan Sin ta gana da babbar jami'ar WHO
2016-07-29 10:28:56 cri

Jiya Alhamis, mataimakiyar firayin ministan kasar Sin Liu Yandong, ta gana da babbar jami'ar hukumar lafiya ta duniya WHO Margaret Chan Fung Fu-chun, da mataimakin babban sakataren MDD, kuma daraktan zartaswar hukumar shirin yaki da cutar AIDs ko Sida ta MDD Michel Sidibe, wadanda ke kai ziyarar aiki a nan birnin Beijing na kasar Sin.

Yayin ganawar tasu, Liu Yandong ta jinjinawa hadin gwiwa dake tsakanin kungiyoyin kasa da kasa da kasar Sin, musamman ma a fannin kiwon lafiya, da aikin shawo kan cutar Sida, kana ta bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kungiyar kiwon lafiyar kasashen duniya, da hukumar shirin cutar AIDs ko Sida ta MDD yadda ya kamata. Ta ce za a yi hakan ne domin kara zurfafa kwaskwarima kan tsarin likitanci na kasar Sin, tare kuma da daga matsayin likitanci da kiwon lafiya na kasashe masu tasowa.

A nasu bangare, Margaret Chan da Michel Sidibe, sun yaba da babban sakamakon da kasar Sin ta samu wajen ci gaban kiwon lafiya, kana sun yi fatan ganin an kara karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, wajen ciyar da hadin gwiwar kiwon lafiya dake tsakanin kasashe masu tasowa gaba cikin lumana, tare kuma da cimma burin samun dauwamammen ci gaba a kasashen.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China