in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin kudin da aka samu daga aikin gandun daji a farkon watanni shida na bana a Sin ya kai yuan biliyan 2580
2016-07-29 10:24:57 cri

A cikin farkon watanni shida na shekarar da muke ciki, sha'anin kara samun wadata ga al'ummar kasa a kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri, inda adadin kudin da aka samu daga aikin gandun daji a fadin kasar ya kai RMB yuan biliyan 2580, adadin da ya karu da kashi 7.7 cikin dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara.

Ban haka, a cikin wadannan watanni shida, fadin itatuwan da aka dasa a kasar ta Sin ya kai hekta 4222, aikin da ya kammala kashi 63.3 cikin dari daga cikin dukkan ayyukan dasa itatuwa a duk shekarar ta bana.

Kaza lika a farkon watanni shida na banan, sha'anin kara samun wadata ga al'ummar kasar ya karu cikin sauri, inda adadin kudin da aka samu daga shigo da kayayyakin gandun daji, da kuma fitar da su zuwa kasashen ketare, ya kai dalar Amurka biliyan 65 da miliyan 200 a kasar ta Sin.

Shugaban hukumar kula da aikin gandun daji ta kasar Sin Zhang Jianlong ya bayyana cewa, tun daga farkon shekarar har zuwa yanzu, aikin gandun daji na kasar Sin ya samu babban sakamako, ciki hadda dasa itatuwa da dama a fadin kasar, da sake gudanar da aikin yaki da kwararowar Hamada da dai sauransu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China