in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO ta yi kira da a tabbatar da ingancin ruwan sha ta hanyar yin amfani da gandun daji
2016-03-22 10:58:54 cri

Kungiyar abinci da aikin gona ta MDD (FAO) ta fara gudanar da shirin "gandun daji da ruwa" a jiya Litinin 21 ga wata, domin jaddada muhimmiyar rawar da gandun daji ke takawa wajen kyautata ingancin ruwan sha.

Babban darektan kungiyar FAO Jose Graziano da Silva ya bayyana a gun bikin murnar ranar gandun daji ta duniya cewa, "a yayin da muke tinkarar kalubaloli daban daban, muna ta nacewa ga kula da gandun daji da albarkatun ruwa masu dorewa."

Mataimakin babban darektan kungiyar FAO mai kula da aikin gandun daji Rene Castro ya ce, "Mun gudanar da wannan shiri ne domin shaida rawar da gandun daji ke takawa wajen warware matsalar karancin ruwa da abinci da kuma inganta karfin yaki da bala'i daga indallahi."

An kuma gabatar da cewa, za a gudanar da wannan shiri a kasashen Nijer, Gambia, Guinea, Guinea-Bissau, Mali, Mauritania, Senegal da Saliyo dake yammacin Afrika, inda kungiyar FAO za ta yi hadin gwiwa tare da su wajen kara musu sani kan huldar dake tsakanin gandun daji da ruwa, da kuma taimake su wajen kara kula da gandun daji a lokacin da ake gudanar aikin gona, domin kyautata aikin samar da ruwan sha.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China