in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saurin raguwar yawan gandun daji na duniya ya ragu da kashi 50 cikin dari, in ji kungiyar FAO
2015-09-08 10:48:33 cri

Hukumar kula da harkokin abinci da aikin gona ta duniya (FAO) bayyana cewa, a cikin shekaru 25 da suka gabata, saurin raguwar gandun daji a duniya ya ragu da kashi 50 cikin dari.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wani rahotonta yayin taron gandun daji na duniya karo na 14 da ya gudana a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu daga ranar 7 zuwa 11 ga wannan wata.

Rahoton ya kara da cewa, a shekarar 1990, fadin gandun daji a duniya ya kai hekta biliyan 4.128, wanda ya dauki kashi 31.6 cikin dari na fadin duniya baki daya.

Amma ya zuwa shekarar 2015, fadin gandun dajin ya ragu zuwa hekta biliyan 3.999, wanda ya dauki kashi 30.6 cikin dari na fadin duniyar mu. Amma a sakamakon kokarin da ake na kafa sabbin gandun dajin, saurin raguwar gandun daji ya ragu da kashi 50 cikin dari ko fiye.

Babban jami'in hukumar FAO Jose Graziano da Silva ya ce, rahoton da hukumar ta fitar ya ba da kwarin gwiwa sosai ga mutane, wanda kuma ya shaida cewa, ana ci gaba da samun karuwar gandun daji kuma yawan iskar gas da ake fitarwa ya ragu.

Bugu da kari, kungiyar FAO ta yi bincike cewa, ana ci gaba da kare wasu gandun daji, kuma karin kasashen duniya suna kyautata aikin kula da gandun daji ta hanyar bullo da dokoki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China