in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Japan da Amurka da Autraliya da su tabbatar da zaman lafiya a Asiya da tekun Pasific
2016-07-28 10:32:27 cri

A jiya Laraba, kasar Sin ta bukaci kasashen Japan da Amurka da Australiya, da su yi abubuwan da suka dace wajen tabbatar da zaman lafiya game da batun tekun kudancin kasar Sin.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin, Lu Kang ya fada a lokacin amsa tambayoyi da aka shirya a ranar Litinin, game da kalaman da kasashen uku suka yi dangane da batun tekun kudancin Sin, ya ce, kasashen uku ba su da wata alaka ta kusa game da batun tekun kudancin Sin.

Lu Kang ya ce, tuni kasar Sin da kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato (ASEAN) suka tsara dokokin da suka dace wajen warware takaddama game da tekun kudancin Sin.

Ya ce, a wasu lokuta kasashen Japan, da Amurka da Autraliya suna kafa hujja ne da dokokin kasa da kasa, amma suna aikata hakan ne da zarar dokokin da aka tsara za su iya biyan muradunsu ne kawai.

Lu, ya jaddada aniyar kasar Sin ta kin amincewa da hukuncin da aka zartar domin biyan bukatar kasar Philippines na kashin kanta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China