in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madagascar ta shawarta a warware batun tekun kudancin Sin ta hanyar tattaunawa kai tsaye
2016-07-08 09:33:04 cri

Gwamnatin tsibirin Madagascar ta ba da shawara kan gudanar da tattaunawar kai tsaye domin warware rikicin tekun kudancin kasar Sin.

Jamhuriyyar Madagascar na nuna goyon bayan bangarorin da rikicin tekun kudancin kasar Sin ya shafa da su bullo da wata tattaunawar kai tsaye tsakaninsu domin zakullo wata hanyar warware matsalar cikin kwanciyar hankali, da kuma kowa zai amince da ita, har ma da warware takadamar kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada, musammun ma bisa tushen kudurori da yarjejeniyoyin shiyyarsu.

Tattaunawa da fahimatar juna kadai ne za su taimaka ga kiyaye zaman lafiya da kwanciyar a wannan shiyya, in ji sanarwar.

Kasar Madagascar na goyon bayan dukkan kasashe dake zabin hanyar yin shawarwarin abokantaka domin karfafa fahimtar juna da karfafa dangantakar kasa da kasa, a cewar wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China