in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na rage talauci ta hanyar yin amfani da irin shuka masu inganci
2016-07-28 10:01:06 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) da AfricaSeeds, hukumar AU dake kula da bangaren irin shuka, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin rage kangin talauci ta hanyar yin amfani da irin shuka masu inganci. Yarjejeniyar za ta ba su damar sake dubawa da sake nazari a fannonin dangantaka hadin gwiwa domin rage talauci a Afrika ta hanyar yin amfani da ire-iren shuka masu inganci domin kara karfin samar da abinci.

Tumusiime Rhoda Peace, komishinan AU dake kula tattalin arzikin karkara da noma, da kuma Kouame Miezan, babban darektan AfrikaSeeds, sun rattaba hannu a ranar Talata a cibiyar kungiyar AU dake birnin Addis Abeba na kasar Habasha.

A yayin bikin rattaba hannun, komishina Tumusiime ya yaba da aikin da AfrikaSeeds ta gudanar wajen kafa wani tsarin dake da manufar ingiza hanyar darajar irin shuka, bunkasa siyasa da manufofin dangantaka, da kuma karfafa sarrafawa da kasuwanci a bangaren aikin hannu na iri a nahiyar Afrika.

Rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar na bayyana wani muhimmin mataki a cikin dangantakarmu da kuma a cikin yunkurin mu na hadin gwiwa na bunkasa aikin noma da rage kangin talauci a nahiyar Afrika, in ji mista Tumusiime. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China