in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ganin cewa, hukuncin da aka yanke game da batun tekun kudancin Sin ba shi da ma'anar doka
2016-07-18 13:39:04 cri

Kwanakin baya masanan da suka halarci taron kara wa juna sani kan dokar kasa da kasa a fannin warware sabani kan 'yancin mallakar yankin teku a yankin Hongkong na musamman na kasar Sin sun bayyana cewa, hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin bai dace da dokar kasa da kasa ba, sannan ba shi da ma'anar doka ko kadan, makasudin yanke hukuncin shi ne cimma wani buri na siyasa ta hanyar facewa da yarjejeniyar dokar teku ta MDD.

Wani farfesa da ke koyar da dokokin kasa da kasa a jami'ar Virginia ta kasar Amurka ya gaya wa manema labarai cewa, kotun da aka kafa bisa bukatar kasar Philippines ta yi watsi da ra'ayin da masanan kasashen duniya suka cimma kan batun, kuma ta yi watsi da hakikanan abubuwan da suke kasancewa cikin dogon lokaci, har ta yanke hukunci cewa, tsibirin Taiping dake tekun kudancin kasar Sin dutse ne ba tsibiti ba ne, hakan ya nuna cewa, kotun ta yi amfani da yarjejeniyar ce bisa son ranta, domin idan kotun ta yanke hukunci cewa, tsibirin Taiping tsibiri ne, to ana iya kafa yankin tattalin arziki mai fadin kafa dubu 1216 ko mita 370600 a kusa da tsibirin, hakan ba zai dace da manufar Philippines ba, lamarin zai shafi batun raba iyakar yankin kasa kan teku tsakanin Sin da Philippines, sai dai wannan ba shi ne abin da ya damun kotun ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China