in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta hallaka mutane 11 a jihar Bornon Najeriya
2016-05-27 10:03:27 cri

Wasu hare hare da mayakan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a kauyukan Gurlum Kwalle, da Jajeri dake Adamari kusa da birnin Maidugurin jihar Borno, sun sabbaba rasuwar mutane 11.

Abba Mohammed, wanda ke aikin sa kai a tawagar tsaro ta 'yan kato da gora, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, maharan sun aukawa kauyukan biyu ne da yammacin ranar Talata. Ya ce, wadanda suka tsira da rayukan su yayin harin sun tabbatar da cewa, ba a sanar da hukumomin tsaro aukuwar lamarin ba a kan lokaci, kasancewar babu hanyar sadarwa ta waya a kauyukan.

Yayin ziyarar jaje da ya kai kauyukan biyu, mataimakin gwamnan jihar ta Borno Usman Durkwa ya ganewa idanun sa halin da ake ciki, inda mazauna yankin suka bayyana masa cewa, cikin wadanda suka rasu hadda mata 3. Tuni kuma aka gudanar da jana'izar bai daya ga mamatan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China