Kasashen Togo da Benin, dake raba tafkin Mono sun dauki niyyar kafa wata hukumar kula da yankin tafkin Mono cikin hadin gwiwa, na shirya wani zaman taron amincewa da nazarin hadin gwiwa dake da nasaba da kafa wani dandalin kungiyoyin fararen hula (OSC) na tafkin Mono a birnin Lome daga ranar 25 zuwa 27 ga wata.
Wannan binciken da cibiyar kula da albarkatun ruwa ta gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (CCRE-ECOWAS) ke yi na da burin tabbatar da samar da dama ga kungiyar fararen hula wajen kafa hukumar kula da tafkin Mono (ABM).
Za a kafa dandalin ne bisa wani matakin halartar kowa, da zai rika la'akari da bukatu da damuwar al'ummomin dake zaune a yankin tafkin Mono.
A cewar masu shiryawa, tunanin kafa wata hukumar kula da tafkin Mono na cikin tsarin aiwatar da shirin shiyya na kula da shigar da albarkatun ruwa dake shafar dukkan kasashe da dukkan kungiyoyin yankin shiyyar. (Maman Ada)