in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu tana dauke da yawan masu ciwon Sida mafi yawa a duniya
2014-04-02 10:28:46 cri

Kasar Afrika ta Kudu tana da mutane kimanin miliyan 6,4 da suka kamu cutar kanjamau a shekarar 2012, adadi mafi girma a duniya, a cewar wani binciken da aka fitar a ranar Talata. Tare da fiye da sabbin mutanen dubu dari hudu dake dauke da wannan cuta a shekarar 2012, kasar Afrika ta Kudu tana a sahun gaba bisa yawan adadin wannan cuta a duniya, in ji wannan bincike.

Adadin wannan cuta ya karu wato ya wuce daga kashi 10,6 cikin 100 a shekarar 2008 zuwa kashi 12,2 cikin 100 a shekarar 2012, a cewar binciken shekarar 2012 kan halayyar mutane, adadin da yaduwarta a cikin kasar Afrika ta Kudu.

Binciken da aka kaddamar a karkashin ministan kimiyya da fasaha, mista Derek Hanekom, da kuma ministan kiwon lafiya na kasar, Aaron Motsoaledi, a yayin wata mahawara ta hanyar majigi a birnin Cape Town na kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China