in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Zimbabwe na kara fuskantar matsaloli, in ji IMF
2016-03-10 09:45:16 cri

Asusun ba da lamuni na kasa da kasa wato IMF a takaice ya yi kira ga mahukuntan kasar Zimbabwe da su gaggauta bullo da managartan manufofin don tsamo tattalin arzikin kasar da ke kara tsunduma cikin mawuyacin hali.

Shugaban tawagar asusun na IMF Dominico Fanizza wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba a lokacin da suka ziyarci kasar, ya ce, duk da cewa, kasar Zimbabwe ta cimma mizanin manufofi da gyare-gyarenta na harkokin kudi, amma tattalin arzikin kasar ya tabarbare sakamakon matsalar fari da karuwar darajar dalar Amurka idan aka kwatanta da kudin kasar Afirka ta kudu, babbar abokiyar cinikayyar kasar ta Zimbabwe.

Don haka jami'in asusun ya ce, kamata ya yi mahukuntan kasar Zimbabwe su gaggauta daukar matakai don ceto tattalin arzikin kasar daga mummunan halin da ya shiga.

Gwamnatin Zimbabwe dai ta yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar zai bunkasa da kaso 2.7 cikin 100 a wannan shekara, akasin hasashen da bankin duniya ya yi na kaso 1.5 cikin 100. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China