in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar MEND a Najeriya ta bukaci tattaunawa da gwamnati
2016-07-11 10:14:50 cri

Kungiyar tsagerun yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya da aka fi sani da MEND ta fada a jiya Lahadi cewa, ta kafa kwamiti wanda zai jagoranci tattaunawar sulhu da gwamnatin kasar.

Jomo Gbomo, shi ne mai magana da yawun kungiyar, ya shedawa kamfanin dillancin labaraun kasar Sin Xinhua cewar, sun ba da wa'adin makonni biyu ga gwamnatin kasar da ta shiga tattaunawa da 'yayanta, domin kawo karshen fasa bututun mai da tsagerun yankin Niger Delta ke kaddamarwa a yankin.

Sai dai MEND ta ambata cewar, ba ta amince ofishin babban mai baiwa shugaban kasar shawara kan al'amurran tsaro ya jagoranci tattaunawar ba, kasancewar mafi yawan batutuwan da suka shafi yankin Niger Delta ba ya cikin dokokin majalisa, kuma wannan tattaunawar sulhu ce ba taro ne na yin bincike ba.

MEND ta bayyana takwararta Niger Delta Avengers (NDA) a matsayin bata gari, wadanda ke neman kudaden fansa daga gwamnati.

A cewar MEND, NDA ta shiga kaddamar da hare hare ne domin son zuciya kawai, da neman abin duniya.

Kungiyar tsagerun ta nuna rashin jin dadinta ga gwamnati mai ci da kamfanonin mai na kasashen waje dake aiki a yankin, bisa abin da ta kira rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla da al'ummomi mazauna yankin, inda a halin yanzu suke bin ma'aikatar kula da yankin Niger Delta (NDDC) biliyoyin kudade da ake warewa yankin.

Kungiyar ta ce, ta dakatar da kaddamar hari kan bututan mai a yankin sama da shekaru biyu da suka gabata, tun lokacin da kungiyar ta sanar da aniyarta ta tsakaita bude wuta kan kayayyakin dake samarwa kasar arziki tun a ranar 30 ga watan Mayun 2014.

A cewar MEND, tun daga lokacin da ta ayyana dakatar da bude wuta, tana ta kokarin neman hanyoyin tattaunawar sulhu na gaskiya da gwamnatin kasar, tare da neman yadda za'a saki wasu daga fursunonin da ake tsare da su na kungiyar da suka hada da Henry da Charles Okah, tare kuma da duba yadda za'a shawo kan matsalar dake addabar yankin na Niger Delta.

MEND ta ce, idan har wa'adin makonni biyun da ta baiwa gwamnatin kasar suka cika, ba ta ji komai daga bangaren gwamnatin ba, kungiyar ta tabbatar gwamnatin shugaba Mohammad Buhari ba da gaske take ba na neman tattaunawa da su, kuma za ta ci gaba da kaddamar da hare harenta ko kuma shiga yajin aiki.

Kungiyar ta yi kaurin suna wajen kaddamar da hare hare kan kamfanonin mai mallakar 'yan kasashen waje dake yankin na Niger Delta, da sace sace, da lalata kayayyaki, da garkuwa da mutane da dai sauransu.

A watan Yunin shekarar 2009 ne, gwamnatin kasar ta yi tayin afuwa ga tsagerun yankin na Niger Delta mai arzikin mai, domin su amince da ajiye makamai, ta yadda za a kawo karshen tashe tashen hankula a yankin, rikicin na matukar haddasawa kasar hasarar biliyoyin daloli na kudaden shiga daga albarkatun mai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China