in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar dattijan Najeriya ta amince da kasafin kudin bana
2014-04-10 09:53:06 cri

Majalissar dattijan tarayyar Najeriya ta amince da kasafin kudin kasar na bana, na naira tiriliyan 4 da miliyan dubu 695, kwatankwacin dalar Amurka miliyan dubu 29 da dari uku.

Majalissar ta amince da kasafin kudin na bana ne a ranar Laraba, watanni hudu da shiga shekarar ta 2014.

Shugaban majalissar ta dattijai David Mark ne dai ya bayyana amincewa da kasafin kudin, bayan yi masa karatu na uku. Ana kuma sa ran sake duba shi a zaman majalissar na ranar Alhamis din nan, kafin gabatar da shi ga shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Wata majiya ta bayyana cewa, ana fatan shugaban kasar zai rattaba hannu kan kasafin kudin a ranar Juma'a 11 ga watan nan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China