Asusun yara na MDD UNICEF, ya bayyana matukar damuwa game da yadda ake samun karuwar mata da yara kanana, wadanda ke shiga hare-haren kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa, an kaddamar da hare-haren kunar bakin wake 27 tsakanin watan Janairu zuwa watan Mayun bana, adadin da ya haura hare-hare 26 na daukacin shekarar bara. Kaza lika cikin jimillar wadannan hare-hare, kaso 75 bisa dari mata da yara kanana ne ke kaddamar da su a wuraren taruwar jama'a.
Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, daga watan Yulin bara, lokacin da aka samu rahoton farko na amfani da mata wajen aikata wannan ta'asa, an samu karin makamantan wadannan hare-hare 9, wadanda 'yan mata da shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 17 suka kaddamar.
UNICEF dai na zargin mai yiwuwa magoya bayan kungiyar Boko Haram, na amfani da yaran da suka tsere wa gidajensu, baya ga wadanda suka yi garkuwa da su, wajen kai hare-haren kunar bakin waken.
Wasu alkaluman da asusun ya fitar sun nuna cewa, akwai yara kusan 10,000 da za su iya fuskantar wannan yanayi, duba da yawan yaran da aka raba da gidajensu, wadanda adadinsu ya kai 743,000, daga jihohi uku da rikicin Boko Haram ya fi shafa. (Saminu)