Kasar Somaliya da kungiyar tarayyar Afrika (AU) na shirin bullo da wasu sabbin darabun tsaro domin taimakawa ga fuskantar barazanar ta'addanci a wannan kasa dake kusurwar Afrika.
Manzon musamman na shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afrika (SRCC) game da kasar Somaliya, mista Francisco Madeira, ya samu ganawa tare da mataimakin firaministan kasar Somaliya, Mohamed Omart Arte, domin tattaunawa batutuwa da suka jibanci ayyukan dake gudana a kasar ta Somaliya. (Maman Ada)