in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta ce aikin 'yan ta'adda ba zai kashe gwiwar yunkurin samar da zaman lafiya a Somaliya ba
2015-08-24 09:56:03 cri

Tawagar kungiyar hada kan kasashen Afrika wato AU dake Somaliya ta yi Allah wadai da harin ta'addaci na ranar Asabar din da ta gabata a birnin Kismayo wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane 16, wasu 30 kuma suka jikkata.

Wakili na musamman dake wakiltar shugaban kungiyar AU a Somaliya Maman Sidikou ya ce, harin da aka kai kan sansanin horas da sabbin sojoji a kasar ba zai dakile yunkurin kungiyar ta AU na ci gaba da aikin samar da zaman lafiya a kasar ta Somaliya ba.

A sanarwar da Sidikou ya fitar a birnin Mogadishu, ya ce, wannan ya nuna karara burin kungiyar Al-Shabaab shi ne rusa kasa, amma ba gina ta ba, sannan ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

Ya kara da cewar, burin kungiyar ta Al-Shabaab shi ne su gurgunta aniyar gwamnatin wajen rusa cibiyar horas da sabbin sojoji wadanda aka dauka aiki, amma ya ce, burinsu ba zai cika ba.

A cewar mista Sidikou, kungiyar ta AU ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma za su ci gaba da kokari har sai sun samar da rundunar soja mai karfi, ta yadda kasar ta Somaliyar za ta zauna da gindinta wajen fuskantar duk wani kalubalen tsaro.

Dama dai kungiyar ta Al-Shabaab ta yi ikirarin daukar naurin harin na baya bayan nan kwanaki kadan bayan fafatawa tsakanin mayakan ta Al-Shabaab da dakarun kasar Somaliya dake samun tallafin sojojin hadin gwiwa na kungiyar ta AU. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China