Rundunar sojojin Uganda ta bayyana a ranar Litinin cewa, sojojin wanzar da zaman lafiya dake kasar Somaliya za su iyar yin aiki da kyau idan aka warware matsalolin da sojojin suke fuskanta a cikin lokaci.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin a birnin Kampala, rundunar sojojin ta bayyana cewa, kasar ta gabatar da damuwarta a yayin wani zaman taro tsakanin manyan jami'an rundunar sojojin kasar da shugaban reshen ayyukan wanzar da zaman lafiya na kwamitin tarayyar Afrika (AU).
Rundunar sojojin Uganda na damuwa sosai kan batun kudadensu na diya, tsaro da kuma kyautatuwar zaman rayuwar sojoji. Haka kuma biyan kudaden alawus na sojoji da aka dage na daga cikin batutuwan taron.
A game da batun biyan kudaden diya, bangaren Uganda ya shawarta wa manyan jami'an AU cewa, ya kamata a kara kudin diya na mutanen da suka mutu da yanzu haka yake dalar Amurka dubu hamsin domin cewa, sojojin da ke mutuwa a kasar Somaliya yawanci suna barin iyalansu cikin rashi, don haka suke bukatar wani karin tallafi, in ji sanarwar.
Mista Bam Sivuyille, shugaban reshen ayyukan wanzar da zaman lafiya, ya bayyana a yayin taron da aka shirya a birnin Nairobi a ranar 31 ga watan Mayu, cewa, jinkirin da ake samu wajen biyan kudaden alawus, na da nasaba da wasu gyare gyaren da aka yi a cikin tsarin kudi na kungiyar AU, kuma hakan ya shafi dukkan sojojin tawagar. (Maman Ada)