Kasar Sin tana son yada al'adunta na hangen nesa wajen warware rikici cikin lumana a rikicin da ake yi yanzu haka a kasar Sudan ta Kudu, in ji Zhong Jianhua, wakilin kasar Sin na musamman a harkokin nahiyar Afrika.
A wata hira ta musamman da ya yi da wakilan Xinhua a jiya Alhamis 2 ga wata a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, Mr. Zhong Jianhua ya ce, Sin ta damu kwarai da al'ammurran da ke faruwa a kasar Sudan ta Kudu, don haka kuma take goyon bayan duk wani kokarin da ake yi na cimma zaman lafiya cikin lumana a kasar.
Wakilin na musamman ya kuma jaddada cewa, matsalar da ta shafi Afrika ya kamata al'ummar nahiyar ne su warware ta da kansu, don haka ne ma Sin a shirye take ta cigaba da yada al'adunta da ta gada na hangen nesa wajen warware rikici domin taimaka wa al'ummar wannan nahiyar warware rikicin cikin gidansu.
Mr. Zhong sai dai ya nuna bukatar dake akwai ta hada kai waje daya a kokarin samar da zaman lafiya da sulhuntawa a tsakanin juna yayin daidaita rikicin da ake yi a kasar Sudan ta Kudu.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a lokacin taronta a Litinin din da ya gabata ya yaba wa kokarin da kasashe masu fada a ji a duniya ke yi, musamman kasar Sin wajen ganin a kawo karshen wannan tashin hankalin. (Fatimah)