in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
BOAD ya amince baiwa Guinea-Bissau rancen kudi na Sefa biliyan 34
2016-07-15 10:35:27 cri

Bankin ci gaban yammacin Afrika BOAD zai baiwa kasar Guinea-Bissau kudin Sefa biliya 34 domin ganin kasar ta gudanar da manyan ayyukan ci gaba, in ji faraministan kasar Baciro Dja, bayan da ya dawo gida da wani rangadin aikin da ya kai a wannan shiyya.

Wadannan kudade za su taimaka musammun ma wajen kafa ayyuka da dama dake shafar inganta noman kwakwar Cajou, wanda ya kasance noman dake kawo kudi ga kasar, da kuma samar da wutar lantarki a wurare 14 na kasar, in ji mista Dja.

A cewarsa, bankin BOAD ya kuma dauki niyyar zuba kudi ga ayyukan bunkasa noman kayan lambu a yankunan Oio da Cacheu dake arewacin kasar, da kuma gyara hanyar mai kilomita 54 dake hada biranen Buba da Catio dake kudanci.

Faraministan Baciro Dja ya kuma bayyana cewa, kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) ita ma tana da wani shirin baiwa kasar Guinea-Bissau kudin Sefa biliya 56. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China