Kwamitin mai wakilan kasashe 15 na MDD, ya bayyana damuwarsa game da tabarbarewar al'amurra na baya bayan nan a kasar ta Guinea-Bissau, tun bayan samun bayanai da kwamitin ya yi game da halin da ake ciki a kasar.
Joao Soares Da Gama, jakadan Guinea-Bissau a MDD, ya sanar da kwamitin tsaro na MDD cewar, kasarsa ta gurgunce sakamakon rikicin siyasar da ya daidaita kasar na dogon lokaci.
A watan da ya wuce, shugaban kasar Guinea-Bissau Jose Mario Vaz ya ayyana Baciro Dja a matsayin sabon firaiministan kasar, lamarin da ya haddasa zazzafar mahawara daga bangaren magoya bayan jam'iyyar PAIGC.
A cewar Soares Da Gama, rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar ya yi matukar haifar da komada ga ci gaban tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)