in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba wa Guinea-Bissau bisa nadin firaminista don samun zaman lafiya a kasar
2015-09-22 10:30:12 cri

A ranar Liltinin din nan kwamitin tsaro na MDD ya jinjinawa kasar Guinea-Bissau sakamakon nada Carlos Correia a matsayin sabon firaministan kasar da cewar hakan tamkar wani mataki ne a kokarin kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.

Shi dai nadin na Mista Carlos wanda aka gudanar a ranar 17 ga wata Satumba wanda kuma mataimakin ne ga shugaban jam'iyyar PAIGC, kuma ita ce jam'iyyar mai rinjaye a majalisar dokokin kasar.

Kwamitin na MDD ya bayyana wannan nadin da cewar, tamkar wani ci gaba ne aka samu na warware rikicin siyasar da kasar ta tsunduma cikin sa tun a tsakiyar watan Agustan wannan shekarar ta 2015.

Kasar wace ta jima tana fama da yawan juyin mulki, ta fada cikin rikicin siyasa ne tun bayan da shugaban kasar Jose Mario Vaz, ya ayyana sauke firaministan kasar Domingoes Simoes Pereira a ranar 13 ga watan Agusta, inda ya maye gurbin sa da Baciro Dja, sai dai Dja, ya yi murabus daga mukamin bayan nada shi da kwanaki 2 bisa umarnin babbar kotun shari'ar kasar.

MDD ta yaba da irin mutunta kundin tsarin mulkin kasar da Guinea Bissau ke nunawa, sa'an nan ta jinjinawa jami'an tsaron kasar sakamakon rashin tsoma baki a harkokin siyasar kasar.

Sa'an nan ta yabawa al'ummar kasar bisa hallar su ta yin la'akari da yanayin siyasar da kasarsu ke ciki.

Kwamitin na MDD ya ce, zai ba da dukkanin goyon bayansa ga wakili na musamman ga babban sakataren MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea Bissau Miguel Trovoada.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China