Kasar Guinea-Bissau ta karyata batun cafke a cikin kasarta sojojin kasar Gambiya dake da hannu a yunkurin juyin mulki kan shugaban kasar Yahya Jammeh. Babu wani sojin kasar Gambiya da ya shigo kasar Guinea-Bissau, kuma jami'an tsaron kasar ba su cafke kowa ba, in ji gwamnatin Guinea-Bissau a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofinta a ranar Lahadi.
Gwamnatin Guinea-Bissau ta bayyana yin allawadai da yunkurin juyin mulkin da ya faru a kasar Gambiya, in ji wannan sanarwa.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Guinea-Bissau ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an cafke wasu sojojin Gambiya uku a kasar Guinea-Bissau. Haka kuma, kungiyar ta yi kashedin tusa keyar wadannan sojoji domin gudun kadda gwamnatin Yahya Jammeh da ba ta girmama 'yancin dan adam ta yanke musu hukuncin kisa. (Maman Ada)