in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta sake jaddada niyyarta ta zama cibiyar makamashi ta shiyyar
2016-07-14 10:55:22 cri
Firaministan kasar Cote d'Ivoire Daniel Kablan Duncan ya bayyana a ranar Laraba a Yamoussoukro, hedkwatar mulkin kasar, cewa yana fatan ganin Cote d'Ivoire ta zama wata cibiyar makamashi a shiyyar yammacin Afrika.

A yayin wata ganawa da kwararru, shugaban gwamnatin Cote d'Ivoire ya yi bayani kan yunkurin kasar mai kyau ta fuskar makamshi.

Daniel Kablan Duncan ya nuna jin dadinsa kan cigaban tattalin arzikin kasar Cote d'Ivoire, tare da bayyana ayyukan da gwamnati ta gudanar da kuma wadanda ake cigaba da aikatawa domin mayar da Cote d'Ivoire, wata kasa mai wadata da kuma fitar lantarki zuwa kasashen shiyyar.

Ya ce, yawan wutar lantarki da ake samarwa ta madatsun ruwa ya karu. Haka zalika an zuba jari sosai a wannan bangare, lamarin da zai taimaka ga kasashe aminai samun wutar lantarki mai inganci a halin yanzu, in ji shugaban gwamnatin.

A cewar Kablan Duncan, kokarin gwamnati na da nufin kara karfin Cote d'Ivoire wajen samar da wutar lantarki. A halin yanzu karfin kasara a wannan fanni ya kai kimanin Megawatt 1.540, wanda ake son kara shi zuwa Megawatt 2.886 a shekarar 2018 da kuma cimma Megawatta 4 zuwa shekarar 2020.

Kasar Cote d'Ivoire na samar da wutar lantarki ga kasashen Ghana, Togo, Benin, Burkina Faso, Mali kuma nan gaba ga kasashen Saliyo, Laberiya da Guinea. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China