in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD zai maida martini muddin wa'adin amincewa da jarjejeniyar zaman lafiya ya kare a Sudan ta Kudu
2015-08-26 10:16:00 cri

Kwamitin sulhun MDD ya yi barazanar daukar matakai a kan shugaban kasar Sudan ta Kudu da zarar yaki amincewa da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya kafin cikar wa'adin a ranar Larabar nan.

Shugabar kwamitin Uche Joy Ogwu, ta tabbatar da hakan ga manema labarai, cewar kwamitin sulhun MDD a shirye yake ya dau matakin gaggawa kan shugaba Salva Kirr muddin ya gaza sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar kafin nan da ranar laraba ta wannan maku.

Ta ce, kwamitin mai mambobi 15 zai dauki matakan gaggawa kan shugaba Kirr ko da kuwa ya amince da sanya hannu kan yarjejeniyar amma ba bisa son ransa ba.

Da aka tambaye ta ko wadanne irin matakai ne za'a dauka kan shugaba Kirr, madam Ogwu ba ta yi karin haske ba, sai ta ce, dama kwamitin ya fara tattaunawa tun da safiyar wannan rana, kan yiwuwar sanya takunkumi kan kasar ta Sudan ta Kudu.

Da take amsa tambayoyi kan batun daukar matakan, Ogwu ta ce, a matsayinta na wakiliyar din din din a majalisar, tana ganin daukar matakin sanya takunkumin jigilar makamai kan kasar zai iya warware matsalar Sudan ta Kudun.

Sai dai ta lura cewar, a yanzu haka, akwai wasu makamai da aka jibge a kasar wadanda kuma akwai bukatar a yi cikakken bayani kansu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China