in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD kan hakkin bil adam ya tura tawagar bincike a Sudan ta Kudu
2015-10-27 10:12:47 cri

Kwamishina mai kula da ayyukan kare hakkin bil adama na MDD Zeid Ra'ad Al Hussein a ranar Litinin din nan ya tura wata tawaga zuwa kasar Sudan ta Kudu domin sun tantance halin da ake ciki na kare hakkin bil adama, sakamakon rahotanni da ke bayyana matsanancin ayyukan take hakkin bil adama da ke wanzuwa daga dukkan bangarorin dake arangama da juna.

A cewar sanarwar da ta fito daga ofishin Mr Zeid, tawagar za ta mai da hankali ne a kan take hakkin bil adama da ake yi, wanda ya shafi fararen hula tun lokacin da fada ya barke a shekara ta 2013. Sannan za'a mika rahoton zuwa ga kwamitin kare hakkin bil adama a zaman taron da za a yi a watan Maris na shekara mai zuwa.

Kwamishinan ya ce, tawagar za ta tantance ayyukan take hakkin bil adama a karkashin dokar kasa da kasa, da kuma dokar jin kai ta kasa da kasa, da wadanda ke da hannu a ciki suka aikata daga dukkan bangarorin dake arangama da juna guda biyu.

Ganin rashin isasshen lokaci da ake da shi, wannan zai zama na share fage ne, za'a dora a kan ayyukan da ofishin kare hakkin bil adama na MDD da ke Sudan ta Kudun suka riga suka yi, sannan zai ba da shawara ga kwamitin kula da hakkin bil adaman a kan matakan da ya kamata su dauka.

Mambobi uku na farko daga cikin mambobi 10 da kwamitin kula da hakkin bil adaman ta nada sun riga sun isa birnin Juba a karshen makon jiya.

Babban kwamishinan ya ce, rahoton bisa ga binciken shi da nazari zai kunshi shawarwari a kan yadda ya kamata a inganta yanayin hakkin bil adama a kasar domin a tabbatar da kowa ya amsa laifin shi na saba ka'ida.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China