in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta amince da kara wa'adin UNMISS a Sudan ta Kudu
2015-10-10 10:02:04 cri

A ranar Juma'ar nan kwamitin tsaro na MDD ya amince da kara wa'adin aikin tawagar samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu wato UNMISS, da nufin aiwatar da kudurorin MDD don warware rikicin da ya dabaibaye kasar.

A yanzu haka, an kara wa'adin shirin na UNMISS zuwa ranar 15 ga watan Disamba. An dai bukaci babban sakataren kwamitin MDD da ya duba rahoton cikin kwanaki 45 domin nazarin irin matakin da ya dace a dauka, musamman batun samar da kayyayakin aiki da kudaden gudanarwa da ake bukata wajen aiwatar da yarjejeniyar da ake sa ran za ta tabbatar da zaman lafiya da kuma warware rikicin na Sudan ta Kudu.

Kwamitin tsaron MDD mai mambobi 15 ya samu amincewar kara wa'adin da kuri'u 13, yayin da kasashe 2 ba su jefa kuri'a ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China