Sudan ta kudu ta musanta rahoton dake cewa, ta rufe ofisoshin jakdancinta na kasashen waje 32, sai dai ta bayyana cewar, a madadin hakan, za ta rage adadin ma'aikatanta sakamakon matsin tattalin arziki da kasar ta tsunduma, a sanadiyyar yakin basasa a kasar har na tsawon shekaru biyu.
A sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce, jaririyar kasar ta fara rage jami'anta dake aiki a ofisoshin jakadanci na kasashen waje
Sanarwar ta kara da cewar, rage ma'aikatan ba ya nufin an rufe ofishin jakadancin ke nan.
Sanarwar ta zo ne bayan wasu rahotannin da ba'a tabbatar da ingancin su ba, wadanda ke nuna cewar, an fara tusa keyar wasu daga cikin jami'an diplomasiyyar daga kasashen wajen saboda gaza biyan kudaden haya kusan watanni 6 saboda durkushewar tattalin arziki.
A shekarar da ta gabata ne, gwamnatin Sudan ta kudun ta rage darajar kudin kasar da kashi 84 cikin 100.
Komadar tattalin arzikin ya faru ne tun bayan da kasar ta tsunduma cikin tashin hankali a watan Disambar 2013.(Ahmad Fagam)