in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alluran rigakafin Ebola da Sin ta samar ingantattu ne, in ji jami'in Saliyo
2015-10-13 09:51:29 cri

Mahukuntan kasar Saliyo sun tabbatar da cewar, alluran rigakafin cutar Ebola da kasar Sin ta samar kuma aka gwada su, an tabbatar da ingancin su.

A cewar jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar lafiya ta kasar Abbas Kamara, ya zuwa yanzu, gwajin da aka gudanar na alluran, ya tabbatar da cewar, ba su da wata illa ga jikin dan-Adam, kuma masu inganci ne.

Ya ce, wadannan allurai za su yi matukar taimakawa gwamnatin kasar a kokarin da take na kawar da cutar baki daya.

An dai fara gwajin samfururin alluran rigakafin cutar Ebolan wanda masana kimiyyar kasar Sin suka kirkira a asibitoci a kasar Saliyo daga ranar 11 ga watan Oktoba.

Kamara ya kara da cewar, cutar Ebola ta zama babbar barazana ga kasar Saliyo, don haka duk wata gudumawar da za ta taimaka wajen kawar da cutar daga doron kasar suna maraba da ita.

Jami'in ya yabawa kasar Sin, kasancewar ita ce kasa ta farko da ta aike magunguna da jami'an kiwon lafiya don taimaka wajen yakar cutar, sannan ta gina katafaren dakin gwajin cutar ta Ebola a kasar ta Saliyo.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China