in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iraki ta kira jakadan Saudiyya bayan wasu kalamai kan mayakan Shi'a
2016-01-25 10:05:05 cri

Hukumomin Bagadaza sun kira a ranar Lahadi jakadan Saudiyya dake kasar domin yin allawadai da kalamansa kan mayakan Shi'a dake yaki da kungiyar IS, kalaman da suka zo tamkar wani shiga sharo ba shanu a cikin harkokin cikin gida na Iraki.

Wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta yi karin haske cewa, dakarun Shi'a da gwamnati take tallafawa, da ake kira Hashd Shaabi, na yaki ne da ta'addanci da kare 'yancin kasa, kuma suna aiki a karkashin gwamnati, ganin cewa, wadannan dakaru na bisa jagorancin mataimakin komanda na rundunar sojojin Iraki.

Kalaman jakadan Saudiya na matsayin wani shisshigi a cikin harkokin cikin gida na Iraki, kuma sun dogara bisa tushen karya, in ji Ahmed Jamal, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iraki.

Jakadan Saudiyya Thamer al-Sabhan ya fadi a ranar Asabar da yamma a cikin wata hira tare da gidan talabaijin na al-Sumaria TV cewa, Kurdawa da mazaunan garin Anbar na watsi da zaman Hashd Shaabi a yankunansu, lamarin dake nuna cewa, dakarun na Shi'a ba su samu karbuwa ba a cikin al'ummar Iraki.

Ko gwamnatin Iraki za ta amince da shigowar mayakan Sunni kamar yadda ake ganin na Shi'a cikin kasar tare da makamai? Kuma me ya sa mayakan Hashd Shaabi ne kawai za su daukar makamai? in ji Thamer al-Sabhan, bisa wannan ayar tambaya.

Haka kuma ya nuna cewa, mayakan da suka aikata kisan jama'a ko luguden wuta kan masallatai na 'yan Sunni a birnin Maqdadiyah dake gundumar Diyala, dake gabashin Iraki, ba su da wani bambanci tare da mayakan kungiyar IS, duk tafiyarsu daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China