Dakarun sojin kasashe 20 ne ke shirin isa kasar Saudiyya, domin gudanar da wani atisayen soji, wanda zai zamo muhimmin aiki na gwada kwarewar rundunonin kasa, da na sama, da kuma na ruwan kasashen.
Atisayen na zuwa ne a daidai gabar da Saudiyyar ke shirin shiga ayyukan soji da kasashen duniya ke gudanarwa domin yaki da kungiyar IS a kasar Syria. Zai kuma zamo wata hanya ta nunawa duniya cewa, saudiyya na da cikakken goyon bayan masu mara mata baya, a kokarin ta na shawo kan kalubalolin da yankin ta ke fuskanta.
Rahotanni na cewa, atisayen zai kasance irin sa mafi girma ta fuskar kasashen da za su halarta, da kuma yawan makaman da za a yi amfani da su a yankin na Gulf.
Za dai a gudanar da atisayen ne a garin Hafr Al-Batin, dake arewacin birnin Riyadh. Zai kuma kunshi kasashen yankin Gulf 6 da suka hada da Saudi Arabia, da Kuwait, da Oman, da hadaddiyar daular Larabawa. Sai kuma kasashen Bahrain da Qatar. Kaza kila ana sa ran halartar sauran kasashe irin su Chadi, da Masar, da Jordan da Malaysia. Sai kuma Morocco, da Pakistan, da Senegal da kuma Tunisiya.(Saminu)