in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana ra'ayinta dangane da batun sulhu tsakanin masu ruwa da tsaki game da tekun kudancin kasar Sin da kasar Philippines ta gabatar
2016-06-30 11:23:58 cri
Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya yi jawabi a ranar Laraba da ta gabata, kan batun yin sulhu tsakanin masu ruwa da tsaki game da tekun kudancin kasar Sin da kasar Philippines ta gabatar.

A cewar kakakin, bisa bukatar da kasar Philippines ta gabatar bisa radin kanta, an kafa wata kotun sulhu kan maganar tekun kudancin kasar Sin, wadda ta sanar a ranar Laraba cewa, za a sanar da hukuncin da aka yanke a karshe a ranar 12 ga watan Yuli mai zuwa. Dangane da batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya nanata cewa, kotun nan da aka kafa ba ta da ikon kula da batun, don haka bai kamata ta gudanar da aikin sulhu gami da yanke wani hukunci ba.

Kakakin ya kara bayyana dalilin da ya sa aka ce kotun ba ta da ikon yanke hukunci, na farko, kasar Philippines ta gabatar da bukatar yin sulhu a wajen kotu kan takaddamar da aka samu tsakanin kasar da bangaren kasar Sin dangane da batun tekun kudancin kasar Sin a ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2013, bukatar da gwamnatin kasar Sin ta ki yarda da ita, har ma kasar ta Sin daga bisani ta nanata wannan matsayin nata sau da dama. Na biyu shi ne, yadda kasar Philippines ta gabatar da batun gaban wata kotun yin sulhu bisa radin kanta, hakan ya zama keta dokokin kasa da kasa ke nan. Dalili na uku shi ne, tun da matakin da kasar Philippines ta dauka bai dace da doka ba, kotun nan da aka kafa ita ma ba ta da ikon kula da batun.

Saboda haka, kakakin ya ce kasar Sin za ta tsaya kan dokokin kasa da kasa, ta yadda za ta yi shawarwari tare da sauran bangarori masu ruwa da tsaki don daidaita batun tekun kudancin kasar Sin yadda ya kamata.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China