in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya bukaci a dauki matakan warware rikicin Darfur ta hanyar siyasa
2016-06-30 09:57:05 cri

Wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci kasashen duniya da su kara daukar matakan da suka dace domin warware rikicin yankin Darfur ta hanyar siyasa.

Liu Jieyi, wanda shi ne wakilin din din din na kasar Sin a MDD, ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan zartar da wani kuduri da kwamitin sulhun MDD ya yi game da tsawaita wa'adin aikin tawagar tarayyar Afrika da MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur UNAMID, zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2017.

Kasar Sin ta yabawa gwamnatin kasar Sudan wajen kokarinta na ingiza zaman lafiyar kasar ta hanyar tattaunawar sulhu, da ci gaban tattalin arzikin kasar da ci gaban yankin na Darfur, har ma da batun kuri'ar raba gardamar da aka gudanar a yankin na Darfur a watan Aprilu.

Liu, ya ce, kasar Sin ta yi maraba da amincewar da gwamnatin Sudan ta yi game da yarjejeniyar da kungiyar tarayyar Afrika ta gabatar ta tabbatar da zaman lafiyar yanki.

Jakadan na Sin ya bukaci kasashen duniya da su sa kaimi wajen gayyato dukkan bangarorin da ba sa ga maciji da juna a yankin da sauran kungiyoyin tada kayar baya na kasar Sudan, domin su sanya hannu kan yarjejejniyar ba tare da bata lokaci ba, domin shiga shirin tattaunawa na yarjejeniyar zaman lafiya ta Doha game da zaman lafiyar Darfur, domin kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye yankin na Darfur.

A ranar 21 ga watan Maris ne, gwamnatin Sudan ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, wadda kungiyar tarayyar Afrika ta gabatar.

Yarjejeniyar dai ta shafi batun tsakaita bude wuta a yankunan da ake fama da rikici a kogin Nilu da kudancin jihohin Kordofan da yankin na Darfur, inda aka bukaci a shiga tattaunawar sulhu. To sai dai kungiyoyin 'yan tada kayar bayan Sudan suna jan kafa game wannan yarjejeniyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China