in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta damu game da halin da ake ciki a arewacin Darfur
2016-02-25 10:04:05 cri

Jami'ar sashen jin kai na MDD a kasar Sudan Marta Ruedas, ta bayyana damuwarta game da halin da 'yan gudun hijira sama da dubu 85 da rikicin arewacin Darfur na kasar Sudan ya raba su da matsugunan su.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya ce, a ranar Litinin da ta gabata, Rueda, ta ziyarci yankin Tawilla dake yammacin El Fasher, inda sama da 'yan gudun hijira dubu 22 ke zaune, kuma mafi yawansu mata ne da kananan yara wadanda rikicin baya bayan nan ya raba su da gidajen su, kuma suna zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira.

Dujarric ya ce, al'ummomi fararen hula suna cikin mawuyacin hali sakamakon tashe tashen hankula a yankunan, amma a cewarsa babban burin MDD shi ne ta ba su kariya.

Bugu da kari, hukumar ba da tallafin jin kai ta MDD OCHA ta fada cewar, akwai kungiyoyin ba da tallafi na kasa da kasa da suke kai kayyayakin tallafi a yankunan, amma sakamakon fuskantar karin tashe tashen hankula, ana fuskantar manyan kalubale ta fuskar ba da agajin.

Dujarri, ya ce, a ranar Talatar da ta gabata, wasu manyan motocin daukar kaya 11 sun tashi daga El Fasher zuwa yankin Sortony dake arewacin Sudan inda a can ne tashin hankalin ya fi kamari, kuma akwai sabbin 'yan gudun hijira sama da dubu 63.

MDD ta bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a tsakiyar Darfur, da su ba da damar shigar da kayayyakin tallafi ga 'yan gudun hijirar da rikicin ya daidaita.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China