in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNAMID ta bukaci masu fada da juna a gabashin Darfur su kai zuciya nesa
2016-04-21 14:07:24 cri

Tawagar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya ta tarayyar Afrika da MDD kan rikicin Darfur (UNAMID) ta bukaci bangarorin da ba sa ga maciji da juna a gabashin Darfur na kasar Sudan da su kai zuciya nesa domin kawo karshen fadan kabilanci da ya daidaita yankin.

UNAMID ta nuna damuwa matuka, sakamakon barkewar sabon fada a yankin wanda ya haddasa kaddamar da hari kan gidan gwamnan lardin Wali in El Daein a ranar Litinin.

Tawagar ta bukaci bangarorin dake yaki da juna da su kaucewa duk wani abun da zai kara gurgunta sha'anin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

UNAMID ta lashi takobin kare rayukan jama'a da kuma tallafawa hukumomin yankin domin samun daidaituwar al'amurra a yankin.

A ranar Litinin ne dai masu dauke da makamai suku afkawa gidan gwamnan lardin, suka cinnawa gidan wuta, sannan suka kashe masu gadi 3.

Wannan lamari ya faru ne kwana guda bayan kashe mutane 12 sakamakon barkewar rikici tsakanin 'yan kabilar Rizeigat da Ma'liya Arab a yankin na gabashin Darfur, rikicin kabilanci a yankin na Darfur ya samo asali ne tun a shekarar 1966.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China