Fiye da yara miliyan biyu suke butatar taimakon jin kai a shekarar 2016 a Chadi, kasar da kuma a lokaci guda take fama da matsalar abinci, hijirar al'ummomi, bukatun kiwon lafiya da kuma bala'u daga indallahi, in ji Gianluca Flamigni, wakilin kungiyar UNICEF a kasar.
Ya jaddada wajabcin mayar da hankali sosai kan kare da ci gaban yara da suka kwashe fiye da rabin al'ummar kasar Chadi.
Ranar yaran Afrika, da aka yi bikinta a wannan shekara bisa taken "Yake yake da rikice rikice a Afrika, kare 'yancin dukkan yara" ta kasance ranar da gamayyar kasa da kasa ta kirkiro domin tunawa da kisan kiyashi na yaran Soweto a kasar Afrika ta Kudu a yayin da suke neman 'yancin samun ilimi mai inganci. Tun daga lokacin, wannan rana ta zama muhimmin lokaci na yin kiraye kiraye domin kare 'yancin yara. (Maman Ada)