in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ware dala miliyan 7 domin taimakawa yankin tafkin Chadi
2016-01-11 10:29:16 cri

Mataimakin sakatare janar na MDD kan harkokin jin kai da agajin gaggawa, Stephen O'Brien, ya amince da bayar da dalar Amurka miliyan 7 daga babban asusun kula da ayyukan gaggawa (CERF) domin samar da agajin jin kai a yankin tafkin Chadi.

Tashe tashen hankali da matsalolin tattalin arziki da na jama'a sakamakon matsalar tsaro a wannan yanki sun tilasta wa fiye da 'yan Chadi dubu 50 ficewa daga tsibiran tafkin Chadi tsakanin watan Yuli da watan Disamban shekarar 2015, domin neman mafaka a wasu sansanonin karbar 'yan gudun hijira kusan goma, kauyuka da unguwanni, da kuma kananan hukumomin Baga-Sola, Bol, Daboua, Kangalom da Liwa, in ji cibiyar kula da ayyukan jin kai ta MDD (OCHA) a cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Jumm'a.

Bayan haka, akwai wasu karin 'yan Chadi dubu 15 da suka dawo daga Najeriya. Wadannan 'yan gudun hijira sun kawo rauni ga sansanonin karbar 'yan gudun hijira da tuni suke fuskantar matsaloli, inda daga cikinsu mutane dubu 112 suke cikin bukata.

Abu na farko na game da wadannan kudade na CERF, shi ne samar da taimakon gaggawa ga dukkan mutanen da matsalar ta shafa, in ji mai kula da aikin jin aiki a kasar Chadi, mista Stephen Tull. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China