Mahukuntan babban bankin Najeriya CBN, sun bayyana aniyar shigar da kasar cikin tsarin biyan kudade na kasa da kasa, tsarin da ke da nagarta, kuma karbabbe ga sauran sassan duniya nan da shekarar 2020.
Babban daraktan bankin na CBN mai lura da harkokin biyan kudade Dipo Fatokun ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin bude taron karawa juna sani na yini biyu, game da harkokin cinikayyar kasashen Turai karo na 5 a birnin ikkon jihar Legas.
Fatokun ya ce, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da sauye-sauye a tsarin biyan kudade a cikin kasar, kuma bankin CBN na fatan aiwatar da muradun kasar a wannan fanni, wadanda aka yiwa lakabi da PSV 2020.
Ya ce, duba da muhimmancin tabbatar da tsarin shigar da kudi da kuma fitar da su kai tsaye, wanda sauran kasashen duniya ke amfani da shi, yanzu haka bankunan kasar sun bi sahun takwarorin su na duniya, wajen fara aiki da wannan tsari, wanda hakan ke kara martabar bankunan Najeriyar a fannin hada-hadar kudade ta kasa da kasa.
Daga nan sai ya jaddada aniyar babban bankin kasar, ta ci gaba da daukar karin matakan bunkasa fasahohin da ake amfani da su, ta yadda bankunan kasar za su kai ga matsayin da ake fata. (Saminu)