in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya yi kashedi game da barazanar koma bayan tattalin arzikin duniya
2015-10-01 13:17:21 cri
Shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF Christine Lagarde ta yi gargadin cewa, tattalin arzikin duniya na dab da shiga wata sabuwar barazanar koma baya na dogon lokaci.

Madam Largade wadda ta bayyana hakan yayin da take jawabi a taron shekara-shekara na IMF da bankin duniya, ta ce, akwai yiwuwar ci gaban tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma baya a wannan shekara, ganin yadda ake samun mabambantan ci gaban tattalin arziki na duniya.

Sakamakon haka, asusun yana fatan rage hasashen da ya yi kan tattalin arzikin duniya a rahotonsa da yake sa ran fitarwa a taronsa na shekara-shekara a Peru cikin mako mai zuwa.

A cewar shugabar asusun na IMF tattalin arzikin kasashen da suka ci gaba zai kama hanyar bunkasa, yayin da kasashen da tattalin arkinsu ke bunkasa kuwa, za su fuskanci koma bayan tattalin arziki na shekaru biyar a jere.

A watan Yuli ne asusun na IMF ya rage hasashen da ya yi game da ci gaban tattalin arzikin duniya da kashi 0.2 cikin 100 zuwa kashi 3.3 cikin 100 inda ya yi fatan tattalin arzikin duniyan zai bunkasa da kashi 3.8 cikin a shekara mai zuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China