in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar IMF ta yi kiran da a rika bin tsarin tafiyar da harkokin kudade
2015-11-06 10:35:25 cri

Shugabar asusun ba da lamuni ta duniya IMF Christine Lagarde ta yi kiran da a dawo da martabar tsarin sarrafa kudade na duniya.

Madam Lagarde wanda ta bayyana hakan a wani taro da baitul malin tarayya na New York na kasar Amurka ya shirya, ta ce wajibi ne tsarin bangaren sarrafa kudade ya kula da dukiyar masu zuba jari ta yadda al'umma za ta samu wadata tare da samar da guraben ayyukan yi.

Ta ce, jama'a na yanke kauna ga tsarin kula da kudade sakamakon yadda wasu ke tabargaza da amanar da jama'a suka damka musu. Inda ta ba da misali da cogen kudin ruwa da farashin kudin musayan da ya faru a kasuwar hada-hadar kudi ta London Whale.

Jami'ar ta IMF ta ce, muddin ana bukatar a daidaita wannan matsala, wajibi ne a samu managarcin tsari tare da bin ka'ida a tafiyar da harkokin kudade.

Don haka, ta yi kiran da a rika amfani da dokar da za a rika hukunta mutanen da suka aikata ba dai-dai ba a sha'anin harkokin kudade. Ta haka ne kadai jama'a za su samu tabbaci kan dukiyar da suka zuba a ko'ina.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China