in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 451 ne aka hallaka tun bayan barkewar rikicin Burundi a Afrilun 2015
2016-05-04 10:08:58 cri

A kalla mutane 451 ne aka tabbatar da mutuwarsu tun bayan barkewar tashin hankali a kasar Burundi, cikin wadanda suka mutu, akwai fararen hula 374 da jami'an 'yan sanda 77, tun bayan fada da ya barke a kasar a watan Afrilun shekarar 2015.

Mai magana da yawun 'yan sandan kasar Burundin Pierre Nkurikiye ya tabbatar da hakan ga manema labaru a Talatar da ta gabata a lokacin gabatar da rahoton karshe na kwamitin bincike da aka kafa wanda ya shafe shekara guda yana tattara bayanai game da rikicin.

Ya ce, rikicin ya samo asali ne a lokacin da jam'iyyun adawa suka yi bore, inda daga bisani suka samu goyon bayan kungiyoyin fararen hular a kasar.

A cewar Nkurikiye, baya ga mutanen da rikicin ya haddasa mutuwarsu, jami'an 'yan sanda 367 ne suka jikkata, sannan fararen hula 368 ne aka raunata.

Ya kara da cewar, jami'an 'yan sanda 12 sun samu nakasa, sannan wasu 8 aka yi garkuwa da su.

Bugu da kari, jami'in ya ce, 'yan sanda 38 ne aka sallama daga aiki sakamakon samun su da hannu wajen aikata munanan laifuka a lokacin rikicin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China