Ministan albarkatun man fetur na Najeriya Ibe Kachikwu, ya fada cewar, danyen man da kasar ta fitar zuwa kasashen ketare ya ragu zuwa kasa da ganga miliyan 1.3 a kowace rana.
Da yake ganawa da manema labaru a Abuja, Kachikwu ya fada cewar, adadin man da ake samarwa ya ragu, amma gwamnatin kasar na ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace domin kara yawan man.
Ya kara da cewar, tabbatar da zaman lafiya a yankin Niger Delta mai arzikin mai ya zama tilas domin dawo da al'amurra yadda ya kamata.
A ranar Litinin gwamnatin Najeriyar ta sanar da aniyarta ta shiga tattaunawa da mayakan yankin Niger Delta.
Gwamnatin ta ce, babban mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro da manyan hafsoshin sojin kasar da shugabannin al'umma da ministan albarkatun man fetur na kasa na daga cikin wadanda za su halarci taron tattaunawar sulhu da mayakan tsagerun yankin na Niger Delta.(Ahmad Fagam)